Tura Ɗalibai 101 Karatu Koyi ne da jagoran Kwankwasiyya – Ɗan majalisar Wudil da Garko

0
277

Dan Majlis tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Wudil da Garko Hon. Abdulhakeem Kamilu Ado, ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin karatu na dalibai 101 da ya dauki nauyin karatunsu a makarantar Kimiyyada da Fasaha ta Jihar Kano.

Ɗaliban da su kaci gajiyar karatun ‘yan asalin yankin na ƙananan hukumomin Wudil da Garko, za su yi karatu a fannin daban-daban a matakin share fagen karatun Diploma, ƙaramar Diploma da kuma Babbar Diploma a makarantar.

An dai ƙaddamar da bikin bawa ɗaliban shaidar fara karatun a safiyar wannan rana ta Talata, 6 ga watan Fabarairu, 2024 da ƙaddamar da sabon shirin sha ka tafi, ga mutane 40.

Da yake jawabi ɗan Majalisar ya bayyana cewa sun bijiro da wannan shirin ne domin koyi da jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso, na canza akalar matasa daga harkokin banga da shaye-shaye zuwa rayuwa mai inganci da ilimi domin kawowa yankinsu gaba.

A cewarsa “ idan ilimi ya zamo yana tasiri a al’ummarmu, sana’a ta zamo itace kan gaba a al’ummar mu bana tunanin nan gaba wani zaiyi gangancin ɗaukar gajeren wando da bokiti ya bawa wani kuma yazo yana godiya akan wannan”.

Ya kuma hori ɗaliban da su zamo jakadu na gari a duk inda su ka tsinci kansu a yayi da kuma bayan kammala karatunsu.

A saƙonsa Gwamnan jihar Kano Eng. Abba Kabir Yusuf, wanda mai taimaka masa na musamman kan harkokin Siyasa Sunusi Surajo Kwankwaso, ya wakilta ya jinjinawa ɗan Majilisar kan wannan abun alkairi tare da tabbatarwa da al’ummar jihar Kano, ƙudirinsu na ciyar da jihar gaba ta fannin Ilimi.

Shima a nasa jawabin shugaban makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Kano, Dr. Abubakar Umar Farouk, ya yabawa ɗan majalisar bisa wannan aikin alkairi da ya dasa wanda al’ummar yankin Wudil da Garko, za su girba har ƙarshen rayuwarsu.

A ƙarshe kimanin mata 40 ne su ka rabauta da sabon shirin Sha ka Tafi, na injinan murjin taliya da ƙaramin buhun Fulawa domin dogaro da kansu kamar yadda ɗan majalisar ya ƙaddamar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here