Bamu Aminta da matakin da ƙasashen mu su ka ɗauba – Al’ummar Mali, Niger da Burkinfaso

0
308

Ƙungiyar dake rajin kare yancin ɗan’adam da Demokraɗiyya wato CISLAC, tare da gamayyar ƙungiyoyi masu alaƙa da ita, sun yi kira da ƙungiyar ECOWAS da ta nemi Shugabannin ƙasashen Mali, Niger da Barkina Faso, domin su sasanta akan batun ficewar su da ga ƙungiyar.

Shugaban ƙungiyar CISLAC Auwal Rafsanjani, ne ya yi wannan kiran a taron ‘yan jaridu da ƙungiyoyin su ka gudanar a babban birnin taraiya Abuja a ranar Alhamis.

Rafsanjani Ya ce ‘’a matsayin su na ƙungiyoyi ma su duba a kan batutuwa da suka shafi jama’a, suna kallon alfanun da ya ke tattare da zaman su na tsintshiya madaurin ki guda, shi ya fi alheri fiye da a ce sun fice da ga cikin kungiyar ta ECOWAS’’.

Rafsanjani ya ƙara da cewa ‘’daga lokacin da aka kafa ƙungiyar ECOWAS a shekara ta 1975, ƙasashen da su ke cikin ta, sun amfana da juna ta hanyoyi da dama, kuma akwai haɗin gwiwa tsakanin su ta fannin tsaro da taimakekeniya a ɓangarori da dama’’.

Ya kara da cewa, ‘’abu mafi mahimmanci a cikin wannan batu, shine wannan ficewa da ƙasashen su ka yi da ga ƙungiyar ECOWAS,ba bu amincewar mutanen da su ke kasashen Niger, da Mali,da Barkina Faso’’.

‘’Shugabannin juyin mulkin ne su ka ce sun fice da ga ƙungiyar’’inji Rafsanjani

Gamayyar ƙungiyoyi sun ce,basa goyon bayan juyin mulkin da shugabannin sojojin su ka yi, sabo da haka su na kira da su da su gaggauta shirya fara zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasashen.

Daɗin daɗawa, gamayyar ƙungiyoyin sun yi kira da ƙungiyar ECOWAS, da ta gaggauta cire takunkumin da aka ɗorawa ƙasar Niger, da sauran ƙasashen domin irin kuncin rayuwa da takunkumin ya saka jama’ar da suke kasashen, musamman mata da yara wadanda ba su su ka yi juyin mulkin ba.

Su ka ce takumkumin ya haramtawa mata da yara da sauran talakawa samun abubuwan more rayuwa, kamar samun kulawa ta fannin asibiti, da samun wutar lantarki da ruwa mai tsafta, da sauran abubuwa da dan adam ya ke buƙata.

Sabo da haka ne su ka yi kira da, Kungiyar ECOWAS da su kasashen da su sasanta da junan su, su koma tsintsiya daya madaurinki guda, domin hakan yafi alheri ga kasashen da al’umar yankin fiye da a ce kowa ya kama gaban sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here