Majalisar Dokokin Kano Ta ce Ba Ta Da Masaniya Kan Bukatar Dawo Da Sanusi a Matsayin Sarkin Kano

0
175

Majalisar dokokin Kano tace bata karanta wata takardar neman rushe masarautun jihar Kano ba.

Tun a ranar Talata wata takarda mai kwanan watan 5 ga Fabrairun shekarar da muke ciki ta karade kafafen sadarwa na zamani.

Takardar wacce wata kungiya mai suna ‘yan Dangwalen jihar Kano ta rubuta ta nemi majalisar dokokin Kano ta rushe masarautun Kano, tare da dawo da sarki Muhammadu Sunusi ii sarautar jihar Kano.

Kungiyar ta nemi majalisar ta sake bibiyar dokar data kafa masarautun Rano, Karaye, Gaya da Bichi wacce gwamnatin data gabata ta Abdullahi Umar Ganduje ta samar.

Sai dai wakilin mu na majalisar dokokin Kano Aminu Abdullahi Ibrahim ya ce tun bayan bullar wannan takarda har kawo yanzu ba a ji an karanta ta a zauren majalisar dokokin Kano ba.

Ko a zaman majalisar na Larabar nan ba a gabatar da wannan takarda ba wanda hakan ke sanya kokonto kan sahihancin ta.

Munyi kuma yi kokarin jin tabakin shugaban kwamitin kananan hukumomi da masarautu Zubairu Hamza Massu, bai dauki kiran da muka yi masa.

Shima mai magana da yawun majalisar Kamaludeen Sani Shawai, ya ce bashi da masaniya kan wannan batu amma zai bincika.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here