AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

0
286

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa birin Abidjan, Côte d’Ivoire don marawa Super Eagles baya a wasan gasar AFCON da ake yi.

Shettima wanda ya tashi ta filin jirgin sama na Abuja, ya tafi kasar don wakiltar Shugaba Bola Tinubu a yunkurin marawa Super Eagles baya.

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasar Stanley Nkwocha ya ce Shettima ya bar Najeriya ne a yammacin Larabar nan.

Ya ce zuwan Shettima Côte d’Ivoire na dauke cikin umarnin Shugaba Bola Tinubu, duka domin marawa Najeriya baya.

Kawo Yanzu haka dai kasa da sa’a guda za a fara wasan da Super Eagles za ta kece raini da Afrika ta Kudu a wasan kusa da karshe a gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

Wasa tsakanin kasashen biyun dai zai gudana A a filin Wasa na Stade de la Paix da ke birnin Bouake a kasar ta Côte d’Ivoire.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here