Tinubu ya bada umarnin sake gina kauyen Tudun Biri dake Kaduna

0
213

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin sake gina garin Tudun Biri baki daya domin samar da ingantattun gidaje ga daukacin mazauna kauyen, sakamakon iftila’in da ya afka musu wanda yayi sanadiyar rasa dimbin rayuka.

Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci kauyen tare da mai baiwa shugaban kasar shawara a kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu domin sake jajanta musu da kuma gabatar musu da wannan albishir.

Sanata Sani yace ana shirya yadda za’a tantance wadanda hadarin ya ritsa da su domin biyansu diyya, yayin da aka sanya malaman addini a ciki domin ganin anyi abinda shari’a ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here