Gwamnatin jihar Kano ta amince ta biya diyyar Naira miliyan dubu 3, ga yan kasuwa da suka mallaki shaguna a filin Idi da aka rusa a watannin baya.
Wannan na kunshe a wata takaddar nema sasanci da aka shigar a ranar 13 ga watan Disambar 2023, a gaban mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da Abuja, bisa amincewar lauyoyin bangaran gwamnati da nay an kasuwar.
Wasu mutum 53 ne suka yi karar gwamnatin Kano a madadin wadanda aka rushe wa shagunan a masallacin Idi.
Masu karar sun gurfanar da hukumar tsara birane ta Kano KANUPDA da kwamishinan shari’a na Kano da mataimakin Sufeton yan sanda na kasa shiyya ta 1 da kuma kwamandan hukumar farin kaya ta Civil Defence a gaban kotun tarayya dake Kano a ranar 29 ga watan Satumba, inda kuma kotun ta umarci gwamnatin Kano ta biya masu shagunan diyyar miliyan dubu 30.
To sai dai bayan kin bin umarnin kotun da gwamnatin Kano ta yi, sai masu korafin suka sake yin karar gwamnatin a gaban kotun tarayya karkashin mai shari’a Inyang Ekwo domin ya tirsasawa gwamnati bin umarnin kotu.
Yayin zaman kotun ranar Alhamis, lauyan masu kara Barrister N. A. Ayagi ya shaidawa kotun cewa lauyoyin gwamnati da na masu kara sun samu cimma matsaya da fahimtar juna, bayan bayanan da yayi lauyan gwamnati Barrister Affis Matanmi bai yi suka ba kan batun.
Hakan ta sa alkalin kotun mai shari’a Ekwo ya yanke hukunci tare da amincewa da matsayar da bangarorin masu kara suka cimma.