Rahotanni daga sassan Najeriya na nuna cewa, farashin albasar da ake amfani da ita wajen girki ya yi tashin goran zabbi, inda ake sayar da buhu guda a kan kudin da ya kama tsakanin naira dubu 120, zuwa dubu 140 a kudancin kasar.
Jihohin Sokoto da Zamfara da Kebbi da Katsina da Kano da Kaduna da kuma Jigawa ne jihohin dake sahun gaba wajen noman albasar a Najeriya, banda wadda ake shigo da ita daga Jamhuriyar Nijar.
Kashin Albasa a Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa
Kashin Albasa a Sabuwar Kasuwar Akinyele dake Ibadan na jihar Oyo a Kudu maso yammacin Najeriya, inda hausawa suka koma bayan rikicin su da yarbawa a Sasa.
Wani manomin albasar a jihar Kano, Alhaji Danladi Umar ya shaidawa Jaridar Daily Trust dalilan da suka sanya karancinta, wadanda ya danganta su da rashin nomata da yawa lokacin damina da kuma matsalar da manomanta ke fuskanta wajen ajiyarta bayan girbi.
Umar yace an noma albasar a jihohin Kano da Kaduna a daminar da ta gabata, amma bukatarta ya zarce abinda aka noma.
Wannan matsayi yayi daidai da na shugaban manoman albasar na jihar Kano, Alhaji Bala Danlarai wanda ya tabbatar da matsalar da suke fuskanta na wuraren ajiyarta bayan girbi da kuma lokacin girbinta wanda kan saba da lokutan da aka fi bukatarta.
Danlarai ya kuma bayyana tsadar albasar da katsewar wadda aka saba shigo da ita daga Jamhuriyar Nijar, yayin da ake fitar da wadda aka noma a Najeriya zuwa kasashen Ghana da Jamhuriyar Benin.
Shugaban manoman yace samar da tsari mai kyau wanda zai taimaka wajen taskance albasar da aka girbe zuwa lokacin da aka fi bukatarta, zai taimaka sosai wajen magance matsalar karancinta da kuma tsadarta