Rundunar ‘yan sanda na bukatar naira biliyan 245 don siyo motocin sintiri-Egbetokun

0
285

Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya ce rundunar ‘yan sanda na bukatar karin kudade da ma’aikata domin magance kalubalen rashin tsaro da aikata laifuka.

Kayode Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a zauren majalisar wakilai ta kasa.

Ya ce ko wane ofis na rundunar na bukatar karin motocin sintiri akalla guda hudu, wadanda za a kashe kimanin Naira biliyan 245 don siyan su.

Ya kara da cewa adadin ‘yan sanda da yawan jama’a a Najeriya ya kai dan sanda 1 yana lura da mutane 1000, wanda ya yi kasa da matakin Majalisar Dinkin Duniya na 1 zuwa 400.

Ya kuma yi kira ga majalisar wakilai da ta tallafa wa ‘yan sanda ta hanyar tabbatar da an basu kudaden da suke bukata, don tabbtar da tsaro tare da kare lafiyar al’ummar kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here