Gwamnatin tarayya za ta fara bawa dalibai bashi daga watan Janairu

0
234

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya ce ana ci gaba da kokarin ganin an fara shirin bayar da bashi ga dalibai a watan Janairun 2024 domin saukaka musu karatu.

Gbajabiamila ya bayyana haka ne a Legas ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da lakca a kwalejin fasaha ta Yaba dake jihar Legas.

Ya ce, A farkon wannan shekarar ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar bayar da lamuni ga dalibai, tare da kafa asusun ba da lamuni na ilimi.

Ya kara da cewa ana ci gaba da shirye-shirye don tabbatar da cewa nan da watan Janairun 2024, daliban Najeriya sun fara karbar bashin.

A cewar Gbajabiamila shirin yazo da sabon tsari, inda dalibai zasu nemi bashin ta hanyar yanar gizo, sannan a tantance su tare da tura musu kudin ta asusun banki, ba kamar yadda aka saba yi a baya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here