Gwamnan jihar Kano, ya nadi Alhaji Abdullahi Musa a matsayin sabon shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar.

0
235

Nadin ya biyo bayan murabus din da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala ya yi bisa radin kansa.

Nadin ya biyo bayan murabus da tsohon shugaban ma’aikata, Alhaji Usman Bala ya yi bisa radin kansa.

Wata sanarwa da Babban Sakataren yada laban gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ta ce, Alhaji Abdullahi Musa Gogaggen ma’aikacin gwamnati wanda ya yi aiki a ma’aikatu da hukumomi daban-daban na sama da shekaru talatin.

Abdullahi Musa ya rike mukamai daban-daban da suka hada da babban sakatare a gidan gwamnatin Kano, daraktan harkokin gudanarwa na ofishin Sakataren gwamnati da sauransu.

Gwamna Abba Kabir ya bukaci sabon shugaban ma’aikatan jihar da yayi aiki tukuru wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here