Matasan APC a Kano, sun bukaci shugaba Tinubu da ya sauke Ganduje a shugaban APC ta Kasa

0
146

Masu girma ‘yan jarida ina maraba da kasancewa tare da ku a wannan lokaci.

Mun tara ku ne a wannan waje a matsayinmu na shugabannin gamayyar kungiyoyin matasan jam’iyyar APC ta Kano, wato kungiyoyin matasa masu kishin kasa da son ci gaban kasa tare da ganin babbar jam’iyyarmu ta APC ta samu nasara a dukkan matakai.

A dai-dai wannan lokaci muna so mu bayyanawa al’umma ra’ayoyinmu kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi yanayin siyasar jihar Kano da kasa baki daya.

1.Muna so mu yi kira ga shugaban kasa kuma Bola Ahmed Tinubu, da ya gaggauta sauke Abdullahi Umar Ganduje daga mukamin shugaban jam’iyyar APC na kasa, saboda gazawarsa wajen ganin APC ta yi nasara a jihar Kano, a zaben gwamna da ya wuce, har ma da rashin nasarar jam’iyyar APC a kotunan karar zabe.

Hakan ya nuna cewa Ganduje ya janyowa APC abun kunya a matakin jiha da kuma kasa baki daya, baya ga zarge-zarge masu karfi da ake dasu a kansa wanda suka shafi cin hanci da rashawa, wanda duk duniya ta shaida.

Haka kuma Ganduje ya ci amanar ‘ya’yan jam’iyyar APC da magoya bayansa a jihar Kano, bisa yadda yayi ta yi musu romon baka da cewa zasu yi nasara a kotu, wanda daga karshe ta tabbata karya yake, bayan da kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin halastaccen gwamnan Kano.

Sannan kuma nadin da aka yi masa na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa ya saba wa tsarin shiyya-shiyya na Jam’iyyar, wanda hakan ya nuna karara cewa ya kamata a baiwa shiyyar Arewa ta tsakiya mukamin Shugaban APC na kasa.

Don haka muna neman Ganduje ya gaggauta sauka daga mukamin, sanan kuma kada Tinubu ya sake ya kara ba shi wani mukami, domin kuwa kara bawa Ganduje wani mukami zai zubar da kima da mutuncin gwamnatin Tinubu a idon duniya.

2. Muna mika sakon jinjina Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) na kasa.

Mun san irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Kano da ma kasa baki daya.

Mun kuma yarda da tasirin farin jininsa da tasirinsa a tsakanin talakawan jihar Kano.

Mun gaskata cewa shi mutum ne mai gaskiya, hangen nesa, da jajircewa.

Don haka muna kira gare shi da ya dawo APC, don kasancewa jagoran APC a jihar Kano, domin kuwa a wannan yanayi da ake ciki shi kadai ne zai iya rike jam’iyyar tare da dawo da martabarta a idon al’umma.

A shirye muke mu yi aiki da shi da kuma mara masa baya a kan manufofinsa na siyasa.

3. A dai-dai wannan gaba, Muna son taya Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano murnar nasarar da ya samu a Kotun Koli.

Mun amince da hukuncin kotun koli kuma mun dauke shi a matsayin kaddara.

Muna rokonsa da ya yi aiki tukuru domin daukaka darajar rayuwar al’ummar Jihar Kano.

Muna ba shi tabbacin hadin kai da goyon bayanmu a kokarinsa na ganin an samar da kyakkyawan shugabanci da romon dimokuradiyya ga al’ummar Jihar Kano.

Daga karshe muna kira ga daukacin al’ummar Jihar Kano, ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba, da su rungumi zaman lafiya da juna, kasancewar dukanmu ’yan’uwa ne, kuma jihar Kano ce a gabanmu.

Muna kira ga al’umma da su nisanci tashin hankali da kalaman batanci, sannan mu karfawa soyayya da taimakon juna, don samun ci gaba mai dorewa a jihar Kano.

Allah ya bamu lafiya da zama lafiya

Nagode

Sadiq Ali Sango

Shugaban Gamayyar Matasan APC Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here