Hukumar kula da aikin hajji ta Kasa NAHCON ta ce daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su koma kayyade farashin kujerar hajji ga maniyyata.
Yayin ganawarsa da wakilan hukumomin alhazai na jihohi da kuma hukumomi masu zaman kansu a birnin Makkah da ke Saudiyya, shugaban NAHCON, Jalala Arabi, ya ce sun dauki sabon matakin bayan ganawa da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya.
NAHCON cikin sabon tsari da ta fitar a Talatar nan, ta ce jihohi ne za su kayyade duk wasu kudade da maniyyatan za su biya wanda zai fara aiki a Hajjin bana.
Hukumar ta yanke shawarar cewa a yanzu kowace jiha za ta kayyade farashinta bisa la’akari da wasu muhimman abubuwa na daiwainiya da alhazai kamar masauki da ciyarwa.
Ta ce daga yanzu an daina biyan kudi bai daya da jihohi za su rika karba daga wajen maniyyata.
Shugaban NAHCON din ya sanar da masu ruwa da tsaki cewa kowace jiha za ta kayyade farashin masauki da ciyarwa domin sanin adadin kudin da maniyyata za su biya.