Hafsat ‘Chuchu’ Ta Musanta Cewa Ita Ta Kashe Nafi’u

0
328

Matar auren nan Hafsat Suraj da aka fi sani da Chuchu, ta shaidawa kotu cewa ba ita ce ta hallaka abokin ta Nafi’u ba.

A baya dai ta shaidawa yan sanda cewa ita ce ta kashe shi bayan ya hana ta kashe kan ta amma a zaman kotu ta musanta hakan.

A Larabar nan ne rundunar yan sandan jihar Kano ta gurfanar da Hafsat Surajo a gaban kotun majistiri mai namba 37 dake zaman ta a Yankaba, bisa zargin ta da aikata laifuka 2 da suka hada da kisan kai da kuma yunkurin kashe kanta.

Haka zalika rundunar ta gurfanar da mijinta mai suna Dayyabu Abdullahi da kuma wani Malam Adamu mai shekaru 65, bisatuhumar su da hada baki da boye gaskiya tare da bayar da bayanan karya.

Daya daga cikin lauyoyin wadanda ake tuhuma, Barrista Rabi’u Sidi, da yake jawabi ga manema labarai bayan fitowa daga kotun, ya ce da aka karanta mata tuhume-tuhumen guda biyu a gaban kotu, Hafsat Surajo ta amsa laifi kan tuhumar farko, amma ta musanta tuhuma ta biyu.

Shi ma barista I.S Abdullahi, lauyan malamin da yan sanda suka kama bisa zargin yi wa mamacin wanka, ya ce wanda yake karewa ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.

Ya ce sun nemi kotu ta bayar da belin waɗanda ake ƙara, amma masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta ba su dama su yi nazarin wannan buƙata, kafin bayar da matsayinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here