Kotun koli ta ce za ta sanar da ranar da za ta yanke hukunci kan shari’ar Kano

0
198

Kotun ƙoli ta jinkirta yanke hukunci kan ƙarar da Gwamna Abba Kabir Yusif ya shigar yana ƙalubalantar hukuncin kotun daukaka kara daya tabbatar da nasarar Dr Nasiru Yusif Gawuna kamar yadda kotun sauraran korafin zabe dake Kano ta yanke. .

Bayan kammala sauraron lauyoyin da suka yiwa kotun bayani game da hujjojin su ciki har da saɗarar data ayyana gwamnan Abba Kabir Yusif a matsayin wanda yayi nasara tare da cin tarar Jamiyyar APC naira miliyan 1 dake kunshe cikin rubutaccen hukuncin da kotun daukaka kara ta fitar, wanda daga bisani tace akwai kura-kurai a ciki.

Kotun kolin mai alkalai 5 karkashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro tace zata bayyana matsayar ta nan gaba kadan bayan nazarin hujjoji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here