Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce babu wani asibiti da yake aiki a Gaza a halin yanzu, musamman arewaci, tana me bayyana damuwa kan halin rashin abinci da ruwa da marassa lafiya ke ciki.
Asibitin Nasser kenan da harin Isra’ila ya lalata a Khan Yunis da ke kudancin Gaza.
Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya, ta tura tawaga ta musamman zuwa wasu asibitoci biyu da harin Isra’ila ya lalata, wato Al-Shifa da kuma Al-Ahli, da ke arewacin Palasdinu.
“Jami’an mu sun gaza bayyana irin halin dimuwar da marasa lafiya da ma’aikatan jinya ke ciki,” in ji wakilin WHO a Palasdinu, Ricahrd Peeperkorn.
Kalaman nassa na zuwa ne, yayin da ake ci gaba da lalubo mafita a diflomasiyyance, domin dakatar da yakin da Hamas ta ce ya lakume rayukan mutum 20,000 a Gaza, kuma kaso 70 daga cikin su mata da kananan yara.
WHO wadda ta bayyana asibitin Al-Shifa, a matsayin mafi girma a Gaza, ya kasance tamkar matattarar matattu a yanzu, yayin da ya fuskancci munanan hare-hare daga dakarun Isra’ila a watan jiya.
Al-Ahli da ya kasance mafi karanci, shine ya ke samun dafifin marasa lafiya da ke karbar kulawar gaggawa har ma da tiyata, inda daraktan asibitin shima ya tsaya cik, sakamakon mamayar da dakarun Isra’ila suka yi masa.