Hukumar Kiyaye Afkuwar Hadura Ta Kasa Ta Baza Jami’ai 1539 Domin Yin Sintiri Yayin Bikin Kirsimeti Da Na Sabuwar Shekara

0
314

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa reshen Kano, ta ce ta baza jami’anta dubu 1 da 500 da 39 domin yin aiki a lokacin bikin kirsimeti da na sabuwar shekara.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban hukumar na jihar Kano, Ibrahim Sallau Abdullahi.

Da yake yiwa Premier Radio karin bayani, Abdullahi Labaran, jami’in hulda da jama’a na hukumar, ya ce sun baza jami’an ne domin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin al’umma gabanin bukukuwan na karshen shekara.

Abdullahi Labaran ya kuma bayyana ka’idojin da ya kamata abi wajen gujewa afkuwar hadura a fadin jihar nan.

Hukumar ta FRSC ta ce za su yi hadin gwiwa da dukkan jami’an tsaro domin tabbatar da tsaro a jihar Kano a lokacin bukukuwan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here