Kotun daukaka kara ta tabbatar da Uba Sani a matsayin zababban gwamnan jihar Kaduna.
A zamanta na yau Juma’a, kotun ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru ya shigar yana ƙalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jam’iyyar APC.