Kotun daukaka kara tace ta soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato.
Kotun ta ce zaben na gwamnan wanda dan jam’iyyar PDP ne bai inganta ba kamar yadda ta bayyana a yau.K
otun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Muftwang tare da ba Goshwe na APC sabuwar takardar shaidar lashe zabe.