Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya bayar da umarnin dakatar da wani malamin makarantar sakandare bisa zargin sa da laifin neman ɗaliba da niyyar lalata.
Hakan na ƙunshe ne a wata takarda da gwamnan ya rubuta wa kwamishinar ilimi a matakin farko ta jihar, Hadiza Yar’adua.
Umarnin gwamnan na zuwa ne bayan samun rahoton cewar malamin, wanda shi ne shugaban makarantar da ke a ƙaramar hukumar Dandume, na neman ɗalibai mata.
Sanarwar wadda ta samu sa hannun daraktan yaɗa labaru na ofishin sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Faskari, ta kuma buƙaci da a yi bincike kan zargin da ake yi wa malamin tare da ɗaukan matakan da suka dace.