Shugaban rudunar sojojin Nigeria Lieutenant General Tapered Lagbaja ya kai ziyarar ta’aziya garin Tudun Biri dake karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

0
379

Shugaban sojojin ya isa garin Tudun Biri ne a Talatan nan tare da jami’an rudunar shelkwatan ciki harda babban kwamandan rudunar soja ta daya dake Kaduna, a inda ya gana da hakimin rigasa Dangaladiman Zazzau Architect Aminu Idris tare shugaban nin al’ummomin yankin.

General Lagbaja ya baiyana alhininshi a game da faruwar ibtila’in kuskuren jefawa al’umman garin Tudun Biri bom, da fatan Allah ya jikansu.

General Lagbaja ya Kara da cewa duk da yakin garin Tudun Biri Yana fama da Yan bindiga a kewaye dashi tun kafin sojoji su fara fatattakarsu sai gashi an samu kuskuren afkawa wadanda basuji ba basu gani ba wannan ba karamin abin takaici bane inji shi.

Da yake mayar da jawabi hakimin rigasa Alhaji Aminu Idris yace yaji dadi da jami’an sojin suka nuna damuwarsu tare da daukar alhakin faruwar lamarin, yace tare da fatan za’a duba wadan suka jikkata tare da iyalai da Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu.

Daga bisani shugaban sojojin tare da sauran jami’an sojin sunyi addu’a ga wadanda suka rasa rayukansu da Kuma fatan wadanda suka jikkata Allah ya basu lafiya, sannan sun ziyace kaburburan da aka birne mamatan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here