Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta miƙa saƙon jajentawa ga ƙasar Namibiya.

0
241

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta miƙa saƙon jajentawa ga ƙasar Namibiya,bisa rasuwar Shugaban kasar Hage Geingob da al’ummar ƙasar baki ɗaya.

Sanarwar na ɗauke da sa hannun Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya Omayuli (Mrs).

Hage Geingob, ya rasu da safiyar jiya Lahadi 4 ga Fabrairu, 2024.

Haka zalika sanarwar ta Bayyana Marigayi Geingob da mai kishin Afirka kuma mai kishin ƙasa wanda za a iya tunawa da irin gudunmawar da ya bayar wajen samun ‘yancin kan ƙasarsa a shekara ta 1990 wanda ya kasance a matsayin jagorar dimokuraɗiyya a Afirka.

Najeriya ta yi baƙin ciki da rasuwarsa kuma ta tsaya tare da Namibiya, a wannan lokaci na baƙin ciki na ƙasa kamar yadda yake kunshe a cikin sanarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here