Ana Zargin Matar Aure Da Kashe Mijinta Da Taɓarya A Gombe

0
467

An dai zargin matar mai matsakaicin shekararu ne wacce ke zaune ne a unguwar Barundare a garin Gombe, babban birnin Jihar da kashe mijin nata mai suna Muhammad Maliki.

Rundunar ce ta sanar da kamun ta bakin Kakakinta, ASP Mahid Mu’azu Abubakar a madadin Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Hayatu Usman.

Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne a ranar 16 ga watan Nuwamban 2023 da misalin karfe 8:21 na dare.

A cewar sanarwar, “Jami’anmu sun samu kiran gaggawa a unguwar Barunde cewar an samu wani ta’asa a wani gida inda ake zargin natar gidan ta kashe mijinta.”

Kakakin rundunar ya ce nan take jami’an su da ke ofishin ’yan sanda na unguwar Low Cost da ke bangaren sashin bincike suka garzaya inda suka tarar da mai gidan kwance male-male cikin jini, inda suka yi gaggawar kai shi asibitin kwararru na Gombe, inda a can likita ya tabbatar da mutuwarsa.

A cewar ’yan sandan, binciken da suka gudanar a lokacin ne ya kai su ga samun nasarar kama matar, wacce suka ce ta amsa cewa ita ta kashe mijin nata.

Sanarwar ta kara da cewa a jawabin Biba da suka dauka ta shaida musu ita ta kashe mijin nata ta hanyar buga masa tabarya a ka, har ya mutu.

Sannan suka ce suna kan ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su tura ta kotu.

Sai dai Biba ta ce ta yi nadamar matakin da ta dauka a kan mijin nata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here