Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce zasu shigar da sabuwar ƙara a kotun koli ta Najeriya kan hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi.

0
554
Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamnan ya ce suna ganin kotun ɗaukaka ƙara bata yi musu adalci ba, amma suna da kyakykyawan fatan kotun koli zata yi musu adalci.

Ya kara da cewa tuni suka umarci lauyoyinsu su shigar da sabuwar kara don kalubalantar hukuncin baya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf yace wannan matsalar da ta faru ta takaitaccen lokaci ce, kuma yana da yakinin kotun ƙoli zata kwatowa alummar Kano hakkinsu.

A ranar juma’a ne kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran kararrakin zaben gwamna a Kano, Inda ta ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC shine halastaccen wanda ya lashe zaben gwamna a Kano na 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here